‏ 1 Chronicles 3

’Ya’yan Dawuda maza

1Waɗannan su ne’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron.

Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;
na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;
2na ukun, Absalom ɗan Ma’aka’yar Talmai sarkin Geshur;
na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;
3na biyar, Shefatiya ɗan Abital;
da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla.

4Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida.

Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,
5kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can.

Shimeya,
Da Ibraniyanci Shimeya, wani suna na Shammuwa
Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa
Bat-shuwa. Waɗansu tsofaffin fassarori biyu (duba kuma 2Sam 11); Ibraniyanci yana da “Batsheba” ne a nan.
’yar Ammiyel ta haifa.
6Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet, 7Noga, Nefeg, Yafiya, 8Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka.

9Dukan waɗannan’ya’yan Dawuda ne maza, ban da’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce’yar’uwarsu.

Sarakuna Yahuda

10Zuriyar Solomon su ne Rehobowam,
da Abiya,
da Asa,
da Yehoshafat,
11da Yoram
Da Ibraniyanci Yoram, wani suna na Yehoram
,
da Ahaziya,
da Yowash,
12da Amaziya,
da Azariya,
da Yotam,
13da Ahaz,
da Hezekiya
da Manasse,
14da Amon,
da Yosiya.
15’Ya’yan Yosiya maza su ne,
Yohanan ɗan fari,
Yehohiyakim ɗa na biyu,
Zedekiya ɗa na uku
Shallum ɗa na huɗu.
16Magādan Yehohiyakim
Da Ibraniyanci Yekoniya, wani suna na Yekoniya; haka kuma a aya 17.
su ne,
Yekoniya ɗansa,
da Zedekiya.

Zuriyar sarauta bayan zaman bauta

17Zuriyar Yekoniya kamamme su ne,
Sheyaltiyel,
18Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.
19’Ya’yan Fedahiya su ne,
Zerubbabel da Shimeyi.
’Ya’yan Zerubbabel maza su ne,
Meshullam da Hananiya. Shelomit ce’yar’uwarsu.
20Akwai kuma waɗansu biyar,
Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed.
21Zuriyar Hananiya su ne,
Felatiya da Yeshahiya, Refahiya, Arnan, Obadiya da Shekaniya.
22Zuriyar Shekaniya su ne,
Shemahiya da’ya’yansa maza. Hattush, Igal, Bariya, Neyariya da Shafat, su shida ne duka.
23’Ya’yan Neyariya maza su ne,
Eliyohenai, Hezekiya da Azrikam, su uku ne duka.
24’Ya’yan Eliyohenai su ne,
Hodawiya, Eliyashib, Felahiya, Akkub, Yohanan, Delahiya da Anani, su bakwai ne duka.
Copyright information for HauSRK