‏ 1 Chronicles 3:1-4

’Ya’yan Dawuda maza

1Waɗannan su ne’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron.

Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;
na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;
2na ukun, Absalom ɗan Ma’aka’yar Talmai sarkin Geshur;
na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;
3na biyar, Shefatiya ɗan Abital;
da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla.

4Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida.

Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,
Copyright information for HauSRK