‏ 1 Chronicles 6

Zuriyar Lawi

1’Ya’yan Lawi maza su ne,
Gershon, Kohat da Merari.
2’Ya’yan Kohat maza su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
3Yaran Amram su ne,
Haruna, Musa da Miriyam.
’Ya’yan Haruna maza su ne,
Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.
4Eleyazar shi ne mahaifin Finehas,
Finehas mahaifin Abishuwa,
5Abishuwa mahaifin Bukki,
Bukki mahaifin Uzzi,
6Uzzi mahaifin Zerahiya,
Zerahiya mahaifin Merahiyot,
7Merahiyot mahaifin Amariya,
Amariya mahaifin Ahitub,
8Ahitub mahaifin Zadok,
Zadok mahaifin Ahimawaz,
9Ahimawaz mahaifin Azariya,
Azariya mahaifin Yohanan,
10Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima),
11Azariya mahaifin Amariya,
Amariya mahaifin Ahitub,
12Ahitub mahaifin Zadok,
Zadok mahaifin Shallum,
13Shallum mahaifin Hilkiya,
Hilkiya mahaifin Azariya,
14Azariya mahaifin Serahiya,
Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak.
15Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.

16’Ya’yan Lawi maza su ne,
Gershom, Kohat da Merari.
17Waɗannan su ne sunayen’ya’yan Gershom.
Libni da Shimeyi.
18’Ya’yan Kohat maza su ne,
Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.
19’Ya’yan Merari maza su ne,
Mali da Mushi.

Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu.
20Na Gershom su ne,
Libni, Yahat,
Zimma,
21Yowa,
Iddo, Zera
da Yeyaterai.
22Zuriyar Kohat su ne,
Amminadab, Kora,
Assir,
23Elkana,
Ebiyasaf, Assir,
24Tahat, Uriyel,
Uzziya da Shawulu.
25Zuriyar Elkana su ne,
Amasai, Ahimot,
26Elkana, Zofai,
Nahat,
27Eliyab
Yeroham, Elkana
da Sama’ila.
28’Ya’yan Sama’ila maza su ne,
Yowel ɗan fari
da Abiya ɗa na biyu.
29Zuriyar Merari su ne,
Mali, Libni,
Shimeyi, Uzza,
30Shimeya, Haggiya
da Asahiya.

Mawaƙan haikali

31Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can. 32Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.

33Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da’ya’yansu maza.

Daga mutanen Kohat akwai,
Heman, mawaƙi
ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,
34ɗan Elkana, ɗan Yeroham,
ɗan Eliyel, ɗan Towa,
35ɗan Zuf, ɗan Elkana,
ɗan Mahat, ɗan Amasai,
36ɗan Elkana, ɗan Yowel,
ɗan Azariya, ɗan Zefaniya
37ɗan Tahat, ɗan Assir,
ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,
38ɗan Izhar, ɗan Kohat,
ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;
39da kuma Asaf’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa.
Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,
40ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya,
ɗan Malkiya,
41ɗan Etni,
ɗan Zera, ɗan Adahiya
42ɗan Etan, ɗan Zimma,
ɗan Shimeyi,
43ɗan Yahat,
ɗan Gershom, ɗan Lawi;
44da kuma daga’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa.
Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi,
ɗan Malluk,
45ɗan Hashabiya,
ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,
46ɗan Amzi, ɗan Bani,
ɗan Shemer,
47ɗan Mali,
ɗan Mushi, ɗan Merari,
ɗan Lawi.

48Aka ba’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah. 49Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.

50Waɗannan su ne zuriyar Haruna,
Eleyazar, Finehas,
Abishuwa,
51Bukki,
Uzzi, Zerahiya,
52Merahiyot, Amariya,
Ahitub,
53Zadok
da Ahimawaz.

(Yoshuwa 21.1-42)

54Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):
55Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta. 56Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne. 57Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa, 58Hilen, Debir, 59Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.
60Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu.
Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.

61Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.
62Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.
63Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.

64Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.

65Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.

66Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.
67A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer, 68Yokmeyam, Bet-Horon, 69Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.
70Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.

71Mutanen Gershom suka sami waɗannan.
Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;
72daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat, 73Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;
74daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon, 75Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;
76daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.

77Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan.
Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;
78daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza, 79Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;
80daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim, 81Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.
Copyright information for HauSRK