‏ 1 Corinthians 11:23-25

Cimar Ubangiji

23Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, 24bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.” 25Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.”
Copyright information for HauSRK