1 Kings 11:41-43
Mutuwar Solomon
(2 Tarihi 9.29-31)
41Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, da dukan abubuwan da ya yi, da hikimar da ya nuna, an rubuta su a littafin tarihin Solomon. 42Solomon ya yi mulki a Urushalima, a bisa dukan Isra’ila, shekaru arba’in. 43Sa’an nan ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Dawuda mahaifinsa. Sai Rehobowam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Copyright information for
HauSRK