2 Chronicles 11:1-4
(1 Sarakuna 12.21-24)
1Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam. 2Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah. 3“Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin, 4‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’ ” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.
Copyright information for
HauSRK