2 Chronicles 22:10-12
Ataliya da Yowash
(2 Sarakuna 11.1-3)
10Sa’ad da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga cewa ɗanta ya mutu, sai ta tashi ta hallaka dukan’yan gidan sarautar Yahuda. 11Amma Yehosheba,’yar Sarki Yehoram, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya ta sace shi daga cikin’ya’yan gidan sarauta waɗanda ake shiri a kashe, ta sa shi tare da mai renonsa a ɗakin kwana. Haka fa, Yehosheba’yar sarki Yoram, matar Yehohiyada firist, ta yi, gama ita’yar’uwar Ahaziya ce, ta ɓoye Yowash don kada Ataliya tă kashe shi. 12Ya kasance a ɓoye tare da su a haikalin Allah shekara shida, yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
Copyright information for
HauSRK