2 Chronicles 3:15-17
(1 Sarakuna 7.15-22)
15A gaban haikalin ya yi ginshiƙai biyu, waɗanda tsawonsu ya kai kamu talatin da biyar, ya yi wa ginshiƙan dajiya, tsayin kowace dajiya kamu biyar ne. 16Ya saƙa sarƙoƙi, ya kuma sa su a bisa ginshiƙan. Ya kuma yi rumman ɗari ya rataya wa sarƙoƙin. 17Ya kafa ginshiƙan a gaban haikalin, ɗaya a kudu, ɗaya kuma a arewa. Ya kira wanda yake kudun, Yakin, ▼▼Yakin wataƙila yana nufin ya kahu.
na arewan kuwa ya kira Bowaz. ▼▼Bowaz wataƙila yana nufin a cikinsa akwai ƙarfi.
Copyright information for
HauSRK