2 Chronicles 7:4-10
4Sai sarki da dukan mutanen suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji. 5Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah. 6Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye. 7Solomon ya tsarkake sashen tsakiya na filin da yake gaban haikalin Ubangiji, a can ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayun salama domin bagaden tagullar da ya yi ba zai iya ɗaukan hadayun ƙonawa, hadayun hatsi da kuma ɓangarori na kitsen ba. 8Ta haka Solomon ya kiyaye bikin a wannan lokaci har kwana bakwai, dukan Isra’ila kuwa tare da shi, babban taro, mutane daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar. 9A rana ta takwas sai suka yi taro, gama sun yi bikin keɓewar bagade na kwana bakwai da kuma biki na ƙarin kwana bakwai. 10A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila.
Copyright information for
HauSRK