2 Kings 11:1-3
Ataliya da Yowash
(2 Tarihi 22.10-12)
1Da Ataliya mahaifiyar Ahaziya ta ga ɗanta ya mutu, sai ta shiga hallaka dukan iyalin gidan sarauta. 2Amma Yehosheba,’yar Sarki Yoram ▼▼Da Ibraniyanci Yehoram, wani suna na Yehoram
,’yar’uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya daga cikin’ya’yan sarkin da ake shiri a kashe, ta ɓoye. Ta ɓoye shi daga Ataliya a wurin mai lura da shi a ɗakin kwana; don kada a kashe shi. 3Ya kasance a ɓoye, shi da mai lura da shi, a haikalin Ubangiji shekara shida yayinda Ataliya take mulkin ƙasar.
Copyright information for
HauSRK