‏ 2 Kings 16:1-4

Ahaz sarkin Yahuda

(2 Tarihi 28.1-27)

1A shekara ta goma sha bakwai ta mulkin Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda ya fara mulki. 2Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba. 3Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a
Ko kuwa ya ma sa ɗansa ya ratsa
wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.
4Ya miƙa hadaya, ya kuma ƙona turare a masujadan tudu, da kan tuddai, da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace.
Copyright information for HauSRK