2 Kings 23:31-34
Yehoyahaz sarkin Yahuda
(2 Tarihi 36.2-4)
31Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki. Ya yi mulki na wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal’yar Irmiya; mutuniyar Libna. 32Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi. 33Fir’auna Neko ya sa shi a sarƙa a Ribla a ƙasar Hamat ▼▼Da Ibraniyanci; Seftuwajin (dubi kuma 2Tar 36.3) Neko a Ribla in Hamat ya cire shi
don kada yă yi mulki a Urushalima, sa’an nan ya sa wa Yahuda harajin talenti ɗari na azurfa, da talenti ɗaya na zinariya. 34Fir’auna Neko ya naɗa Eliyakim ɗan Yosiya sarki a maimakon mahaifinsa, ya kuma canja masa suna zuwa Yehohiyakim. Ya ɗauki Yehoyahaz ya kai Masar, a can ya mutu.
Copyright information for
HauSRK