‏ 2 Kings 24:18-20

Zedekiya sarkin Yahuda

(2 Tarihi 36.11-16; Irmiya 52.1-3)

18Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal’yar Irmiya; mutuniyar Libna. 19Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi. 20Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa.

Fāɗuwar Urushalima

To, sai Zedekiya ya yi wa sarkin Babilon tawaye.
Copyright information for HauSRK