2 Samuel 22
Waƙar yabo da Dawuda ya yi
(Zabura 18.2-50)
1Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu. 2Ya ce, “Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;3Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya
shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona.
Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona.
Daga mutane masu fitina, ka cece ni.
4“Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
na kuwa tsira daga abokan gābana.
5Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni;
raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.
6Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni;
tarkuna kuma suka auka mini.
7“A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;
na yi kira ga Allahna.
Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata;
kukata ta zo kunnensa.
8Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza,
harsashan sararin sama sun jijjigu;
suka yi makyarkyata saboda yana fushi.
9Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa;
harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa,
garwashi mai ƙuna daga bakinsa.
10Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,
girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa.
11Ya hau kerubobi, ya tashi sama;
ya yi firiya a fikafikan iska.
12Ya mai da duhu abin rufuwarsa
gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.
13Daga cikin hasken gabansa
garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya.
14 Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama;
aka ji muryar Mafi Ɗaukaka.
15Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba,
da walƙiya kuma ya sa suka gudu.
16Aka bayyana kwarin teku,
tushen duniya suka tonu.
A tsawatawar Ubangiji,
da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.
17“Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni,
ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye.
18Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko,
daga maƙiyina da suka fi ƙarfina.
19Suka auka mini cikin ranar masifata,
amma Ubangiji ya kiyaye ni.
20Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi;
ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.
21“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina;
bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.
22Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji;
ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.
23Dukan dokokinsa suna a gabana;
ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.
24Ba ni da laifi a gabansa
na kiyaye kaina daga yin zunubi.
25 Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina
bisa ga tsarkina a gabansa.
26“Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci,
ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,
27ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki.
Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.
28Kakan ceci mai tawali’u,
amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.
29Ya Ubangiji kai ne fitilata;
Ubangiji ya mai da duhuna haske.
30Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji;
tare da Allahna zan iya hawan katanga.
31“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce;
maganar Ubangiji babu kuskure.
Shi garkuwa ce
ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.
32Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba?
Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?
33Allah ne ya ba ni ƙarfi,
ya kuma mai da hanyata cikakkiya.
34Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa;
ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.
35Ya hori hannuwana don yaƙi,
hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
36Ka ba ni garkuwar nasararka;
ka sauko don ka sa in sami girma.
37Ka fadada hanya a ƙarƙashina
domin kada idon ƙafana yă juya.
38“Na fafari abokan gābana, na murƙushe su;
ban kuwa juya ba sai da na hallaka su.
39Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba,
sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna.
40Ka ba ni ƙarfi don yaƙi;
ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.
41Ka sa abokan gābana suka juya a guje,
na kuwa hallaka maƙiyina.
42Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su,
suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.
43Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura;
na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna.
44“Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena;
ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai.
Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina,
45baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci;
da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya.
46Zukatansu ta karaya;
suka fito da rawan jiki daga kagararsu.
47“Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena!
Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!
48Shi ne Allahn da yake rama mini,
wanda ya sa al’ummai a ƙarƙashina,
49wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina.
Ka ɗaukaka ni bisa maƙiyina;
ka kiyaye ni daga hannun mugayen mutane.
50Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai;
Zan rera waƙoƙin yabo ga sunanka.
51“Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara;
ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa,
ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”
Copyright information for
HauSRK