‏ Ecclesiastes 10

1Kamar yadda matattun ƙudaje sukan ɓata ƙanshin turare,
haka’yar wauta takan ɓata hikima da daraja.
2Zuciyar mai hikima takan karkata ga yin abin da yake daidai,
amma zuciyar wawa takan karkata ga yin mugun abu.
3Ko yayinda yake tafiya a kan hanya
wawa yakan nuna cewa ba shi da hankali,
yakan nuna wa kowa wawancinsa.
4In hankalin mai mulki ya tashi game da kai,
kada ka bar inda kake,
gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.

5Akwai muguntar da na gani a duniya,
irin kuskuren da yake fitowa daga masu mulki.
6Akan sa wawaye a manyan matsayi,
yayinda masu arziki suna ƙarƙashi.
7Na taɓa ganin bayi a kan dawakai,
yayinda’ya’yan sarki suna takawa a ƙasa kamar bayi.

8Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki;
duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara.
9Duk mai farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni;
duk mai faskaren itace yana cikin hatsarinsu.

10In gatari ya dakushe
ba a kuma wasa shi ba,
dole a yi amfani da ƙarfi da yawa,
amma ƙwarewa yana kawo nasara.

11In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi,
ina amfanin maganin?

12Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne,
amma maganganun wawa za su hallaka shi.
13Farkon maganarsa wauta ce,
ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka,
14wawa kuma yakan yi ta surutu.

Ba wanda ya san abin da zai zo
wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?

15Aikin wawa yakan gajiyar da shi,
har bai san hanyar zuwa gari ba.

16Kaitonki, ya ke ƙasa wadda sarkinki bawa ne
Ko kuma sarki yaro ne

wadda kuma hakimanta ke ta shagali tun da safe.
17Mai albarka ce, ya ke ƙasa wadda sarkinki haifaffen gidan sarauta ne,
wadda hakimanta suke samun abincinsu a daidai lokacin
don samun ƙarfi ba don buguwa ba.

18In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa,
in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.

19Akan shirya abinci don jin daɗi,
ruwan inabi kuwa don faranta zuciya,
amma kuɗi ne amsar kome.

20Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne,
ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne,
gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka,
tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.
Copyright information for HauSRK