Exodus 15
Waƙar Musa da Miriyam
1Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan rera waƙa ga Ubangijigama an ɗaukaka shi ƙwarai.
Doki da mahayinsa
ya jefa su cikin teku.
2“Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
ya zama cetona.
Shi Allahna ne, zan yabe shi.
Allah na kakana, zan ɗaukaka shi.
3 Ubangiji mai yaƙi ne
Ubangiji ne sunansa.
4Karusan Fir’auna da sojojinsa
ya jefa cikin teku.
Zaɓaɓɓun jarumawansa ya nutsar da su cikin Bahar Maliya.
5Zurfafan ruwaye sun rufe su;
suka nutse cikin zurfi kamar dutse.
6Hannun damanka, ya Ubangiji,
Mai kwarjini ne da iko,
hannun damanka, ya Ubangiji,
ya farfashe magabci.
7“A cikin girman kwarjininka
ka kā da waɗanda sun yi gāba da kai.
Ka aiki fushinka mai zafi
ya cinye su kamar tattaka.
8Da hucin numfashin hancinka
ruwaye suka tattaru.
Ruwaye masu kwararowa, suka tsaya kamar bango;
ruwaye na zurfafa suka daskare a tsakiyar teku.
9Magabci ya yi fahariya, cewa
‘Zan fafare su, in ci musu.
Zan raba ganima;
abin da na so ya samu.
Zan ja takobina
hannuna kuwa zai hallaka su.’
10Amma ka hura numfashinka
sai teku ya rufe su.
Suka nutse kamar darma
cikin manyan ruwaye.
11Wane ne cikin alloli,
ya yi kamar ka, ya Ubangiji?
Wane ne kamar ka,
mai ɗaukaka cikin tsarki,
mai banrazana cikin ɗaukaka,
mai aikata al’ajabai?
12“Ka miƙa hannunka na dama,
ƙasa ta haɗiye abokan gābanka.
13A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe
mutanen da ka fansa.
A cikin ƙarfinka, za ka bishe su
zuwa mazauninka mai tsarki.
14Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki
tsoro zai kama mutanen Filistiya.
15Sarakunan Edom za su tsorata,
shugabannin Mowab za su yi rawar jiki,
mutanen Kan’ana za su narke.
16Razana da tsoro za su fāɗo a kansu.
Da ikon hannunka
za su tsaya cik kamar dutse,
har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.
17Za ka kawo su, ka dasa su
a kan dutsen nan naka
inda, ya Ubangiji, ka shirya domin mazauninka,
wuri mai tsarkin da hannuwanka suka kafa, ya Ubangiji.
18“Ubangiji zai yi mulki
har abada abadin.”
19Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa. 20Sa’an nan Miriyam annabiya,’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa. 21Miriyam ta yi musu waƙa. “Ku rera ga Ubangiji
gama ya ci gawurtacciyar nasara.
Doki da mahayi,
ya jefa cikin teku.”
Ruwayen Mara da Elim
22Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba. 23Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara). 24Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?” 25Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi. A can Ubangiji ya yi musu doka da farilla, a can kuma ya gwada su. 26Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.” 27Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.
Copyright information for
HauSRK