‏ Exodus 23:14-17

Bukukkuwa uku na shekara

(Fitowa 34.18-26; Maimaitawar Shari’a 16.1-17)

14“Sau uku a shekara za ku yi mini biki.

15“Ku yi Bikin Burodi Marar Yisti, kwana bakwai za ku ci burodi marar yisti, kamar yadda na umarce ku. Ku yi wannan a lokacin da aka ayana a watan Abib, gama a watan ne kuka fito daga Masar.

“Kada wani yă zo a gabana hannu wofi.

16“Ku yi Bikin Girbi da nunan fari na amfanin shuke-shuken gonarku.

“Ku yi Bikin Tattarawa a ƙarshen shekara, sa’ad da kuka tattara amfani daga gonarku.

17“Sau uku a shekara, maza duka za su bayyana a gaban Ubangiji Mai Iko Duka.
Copyright information for HauSRK