‏ Exodus 29:38-43

(Firistoci 6.8-13; Ƙidaya 28.1-8)

38“Ga abin da za ka miƙa a bisa bagaden kowace rana.’Yan raguna biyu masu shekara ɗaya-ɗaya. 39Ka miƙa ɗaya da safe, ɗaya kuma da yamma. 40Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha. 41Ka miƙa ɗaya ragon da yamma, tare da hadaya ta gari da hadaya ta sha kamar aka yi ta safe, mai daɗin ƙanshi, wato, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.

42“Wannan za tă zama hadaya ta ƙonawar da za a dinga yi kowace rana, daga tsara zuwa tsara. Za a yi ta miƙa hadayar a ƙofar Tentin Sujada a gaban Ubangiji. A can zan sadu da kai, in yi magana da kai; 43a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata.
Copyright information for HauSRK