Exodus 35:4-9
Kayayyaki don tabanakul
(Fitowa 25.1-9; 35.10-19)
4Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta. 5Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta,“zinariya, azurfa da tagulla;6shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin,
da gashin akuya;
7fatun rago da aka rina ja, da fatun shanun teku; da itacen ƙirya
8da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi;
9duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
Copyright information for
HauSRK