‏ Exodus 36:35-38

(Fitowa 26.31-37)

35Suka kuma yi labule da shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, suka kuma yi wa labulen zānen kerubobi na gwaninta. 36Suka yi dogayen sanduna huɗu na itacen ƙirya dominsa, suka dalaye su da zinariya. Suka yi ƙugiya na zinariya dominsa, suka yi rammuka huɗu da azurfa. 37Suka yi wa ƙofar tenti labulen shuɗi, shunayya, jan zare, da kuma lallausan lilin, aikin gwaninta; 38suka kuma yi dogayen sanduna biyar da ƙugiya dominsu. Suka dalaye saman dogayen sandunan da abin daurinsu da zinariya, suka kuma yi rammukansu guda biyar da tagulla.
Copyright information for HauSRK