Exodus 37:25-28
Bagaden ƙona turare
(Fitowa 30.1-5)
25Suka yi bagaden ƙona turare da itacen ƙirya. Shi bagaden, murabba’i ne, tsawonsa kamu ɗaya, fāɗinsa kamu ɗaya, tsayinsa kuma kamu biyu, ƙahoninsa kuwa a haɗe suke da shi. 26Suka dalaye saman da dukan gefe-gefen da kuma ƙahonin da zinariya zalla, suka kuma yi zubin zinariya kewaye da shi. 27Suka yi zobai biyu na zinariya a ƙarƙashin zubin, biyu-biyu ɗaura da juna, don su riƙe sandunan da za a ɗauka shi. 28Suka yi sandunan da itacen ƙirya, suka kuma dalaye su da zinariya.
Copyright information for
HauSRK