‏ Exodus 39:22-26

Sauran rigunan firistoci

(Fitowa 28.31-43)

22Suka kuma saƙa taguwa ta efod da shuɗi duka, aikin gwani mai saƙa, 23an yi wa taguwar wuyan wundi a tsakiya kamar sulke, aka daje wuyan don kada yă kece. 24Suka yi fasalin’ya’yan rumman da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da lallausan lilin kewaye da gefe-gefen taguwar. 25Suka yi ƙararrawa da zinariya zalla, suka sa su a tsakanin fasalin’ya’yan rumman kewaye da gefe-gefen taguwa. 26Aka jera ƙararrawan da’ya’yan rumman bi da bi. Haka aka jera su kewaye da gefe-gefen taguwar aiki, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Copyright information for HauSRK