‏ Ezekiel 19

Makoki domin sarakunan Isra’ila

1“Ka yi makoki game da sarakunan Isra’ila 2ka ce, “ ‘Mahaifiyarki zakanya ce
cikin zakoki!
Takan kwanta cikin’yan zakoki
ta kuma yi renon kwiyakwiyanta.
3Ta goyi ɗaya daga cikin kwiyakwiyanta,
ya yi girma ya zama zaki mai ƙarfi.
Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta
yakan kuma cinye mutane.
4Al’ummai suka ji labarinsa,
aka kuma kama shi cikin raminsu.
Suka ja shi da ƙugiyoyi
zuwa ƙasar Masar.

5“ ‘Sa’ad da ta ga sa zuciyarta bai cika ba,
abin da take fata gani ya tafi,
sai ta ɗauki wani daga cikin kwiyakwiyanta
ta mai da shi zaki mai ƙarfi.
6Ya yi ta yawo a cikin zakoki,
gama yanzu shi zaki ne mai ƙarfi.
Ya koyi yayyage abin da ya yi farauta
yakan kuma cinye mutane.
7Ya rurrushe kagaransu
ya kuma ragargaza biranensu.
Ƙasar da dukan waɗanda suke cikinta
sun tsorata da jin rurinsa.
8Sai al’ummai suka tayar masa,
waɗannan daga yankunan da suke kewaye.
Suka yafa raga dominsa
ya kuwa fāɗa cikin raminsu.
9Da ƙugiyoyi suka ja shi cikin keji
suka kawo shi wurin sarkin Babilon.
Suka sa shi cikin kurkuku,
saboda haka ba a ƙara jin rurinsa
a kan duwatsun Isra’ila ba.

10“ ‘Mahaifiyarku kamar kuringa ce a cikin gonar inabi
da aka shuka kusa da ruwa;
ta ba da’ya’ya da kuma cikakkun rassa
saboda yalwan ruwa.
11Rassanta suka yi ƙarfi,
suka dace da sandar mai mulki.
Ta yi tsayi
zuwa sama
ana ganin ta saboda tsayinta
da kuma saboda yawan rassanta.
12Amma aka tumɓuke ta cikin fushi
aka jefar da ita a ƙasa.
Iskar gabas ta sa ta yanƙwane,
aka kakkaɓe’ya’yanta;
rassanta masu ƙarfi suka bushe
wuta kuma ta cinye su.
13Yanzu an shuka ta a hamada,
a busasshiyar ƙasa marar ruwa.
14Wuta ta fito daga jikin rassanta
ta cinye’ya’yanta.
Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta
da ya dace da sandar mai mulki.’

Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”
Copyright information for HauSRK