‏ Ezekiel 30

Makoki domin Masar

1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2“Ɗan mutum, ka yi annabci ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Yi kuka kana cewa,
“Kaito saboda wannan rana!”
3Gama ranar ta yi kusa,
ranar Ubangiji ta gabato,
ranar gizagizai,
lokacin hallaka wa al’ummai.
4Takobi zai zo a kan Masar,
azaba za tă zo a kan Kush.
Sa’ad da kisassu za su fāɗi a Masar,
za a kwashe dukiyarta a tafi
a rushe harsashinta.

5Kush da Fut, Lidiya da dukan Arabiya, Libiya
Da Ibraniyanci Kub
da kuma mutanen ƙasar alkawari za su mutu ta wurin takobi tare da Masar.

6“ ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “ ‘Waɗanda suke goyon bayan Masar za su fāɗi
ƙarfinta da take fariya da shi zai ƙare.
Daga Migdol zuwa Aswan
za su mutu ta wurin takobi a cikinta,
in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
7Za su zama kango
a cikin ƙasashen da suke kango,
biranensu kuwa za su zama kufai
a cikin biranen da suka lalace.
8Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji,
sa’ad da suka ga na sa wuta wa Masar
aka kuma ragargaza masu taimakonta.

9“ ‘A wannan rana manzanni za su fito daga wurina a jiragen ruwa don su tsorata Kush daga sake jikinta. Azaba za tă kama su a ranar hallakar Masar, gama tabbatacce za tă zo.

10“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan kawo ƙarshen mutanen Masar
ta hannun Nebukadnezzar sarkin Babilon.
11Shi da sojojinsa, mafi bantsoro cikin al’ummai,
za a kawo don su hallaka ƙasar.
Za su zāre takuba a kan Masar
su kuma cika ƙasar da kisassu.
12Zan kafe rafuffukan Nilu
in sayar da ƙasar ga mugayen mutane;
ta hannun baƙi
zan sa ƙasar ta lalace da kome da yake cikinta.

Ni Ubangiji na faɗa.

13“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Zan hallaka gumaka
in kuma kawo ƙarshen siffofi a Memfis.
Da Ibraniyanci Nof; haka ma a aya 16.

Ba za a ƙara samun yerima a ƙasar Masar ba,
zan kuma baza tsoro a duk fāɗin ƙasar.
14Zan lalace Masar ta Bisa
Da Ibraniyanci lalace Faturos

in ƙuna wuta wa Zowan
in zartar da hukunci a kan Tebes.
Da Ibraniyanci No; haka ma a ayoyi 15 da 16.

15Zan kwarara hasalata a kan Felusiyum,
Da Ibraniyanci Sin; haka ma a ayar 16.

kagarar Masar,
in kuma datse mutanen Tebes.
16Zan ƙuna wuta wa Masar;
Felusiyum za tă sha azaba mai zafi.
Za a tayar wa Tebes da hankali;
Memfis za tă riƙa kasance cikin ɓacin rai.
17Samarin Heliyofolis
Da Ibraniyanci Awen (ko On).
da Bubastis
Da Ibraniyanci Fi Beset

za su mutu ta wurin takobi,
biranen kansu za su tafi bauta.
18Duhu ne zai zama rana a Tafanes
sa’ad da na karye ikon Masar;
a can ƙarfin da take fariya zai ƙare.
Za a rufe ta da gizagizai
ƙauyukanta kuma za su tafi bauta.
19Ta haka zan zartar da hukunci a kan Masar,
za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

An Ƙarye Hannuwan Fir’auna

20A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na fari a rana ta goma sha bakwai, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 21“Ɗan mutum, na karye hannun Fir’auna sarkin Masar. Ba a daure shi don warkarwa ba ko a sa tsinke saboda kada yă zama da ƙarfi har ya riƙe takobi. 22Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da Fir’auna sarkin Masar. Zan karye hannuwansa biyu, hannun da yake da kyau da kuma wanda an riga an karya, in kuma sa takobi ya fāɗi daga hannunsa. 23Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. 24Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon in kuma sa takobina a hannunsa, amma zan karya hannuwan Fir’auna, zai kuwa yi nishi a gabansa kamar mutumin da aka yi wa raunin mutuwa. 25Zan ƙarfafa hannuwan sarkin Babilon, amma hannuwan Fir’auna za su shanye. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na sa takobi a hannun sarkin Babilon na kuma miƙa shi a kan Masar. 26Zan watsar da Masarawa a cikin al’ummai in warwatsa su cikin ƙasashe. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
Copyright information for HauSRK