‏ Ezekiel 31

Al’ul a Lebanon

1A shekara ta goma sha ɗaya, a wata na uku a rana ta farko, maganar Ubangiji ta zo mini cewa, 2“Ɗan mutum, faɗa wa Fir’auna sarkin Masar da jama’arsa cewa, “ ‘Da wa za a kwatanta girmanka?
3Ka dubi Assuriya, ta taɓa zama kamar al’ul a Lebanon
da rassa masu kyau suna inuwartar da kurmi;
ya yi tsayi ainun
kansa ya kai cikin gizagizai.
4Ruwa ya sa ya yi girma,
zurfafan maɓulɓulai sun sa ya yi tsayi;
rafuffuka suna gudu
kewaye da tushensa
yana aika da rafuffukansa
zuwa dukan itatuwan kurmi.
5Saboda haka ya yi tsayi
fiye da sauran itatuwan kurmi;
rassansa suka ƙaru
suka yi tsayi,
suka bazu saboda yalwar ruwaye.
6Dukan tsuntsayen sararin sama
suka yi sheƙa a rassansa,
dukan namun jeji
suka haihu a ƙarƙashin rassansa;
dukan al’ummai
suka zauna a inuwarsa.
7Yana da girma a kyau,
da dogayen rassansa da ya baza,
gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa
har cikin yalwar ruwaye.
8Al’ul a cikin lambun Allah
ba su kai shi ba,
balle itatuwan kasharina
su kai rassansa,
ko itatuwan durumi
su kai rassansa,
ko itace a lambun Allah
ya kai kyansa.
9Na sa ya yi kyau
da yalwar rassa,
abin ƙyashi na dukan itatuwan Eden
a lambun Allah.

10“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin ya yi tsayi, kansa kuma ya kai cikin gizagizai, kuma domin ya yi fariya saboda tsayinsa, 11na miƙa shi ga mai mulkin al’ummai, don yă sāka masa gwargwadon muguntarsa. Na jefar da shi a gefe, 12kuma baƙi mafi mugunta na al’ummai suka sare shi suka bar shi. Rassansa sun fāɗi a kan duwatsun da suke cikin dukan kwaruruka; rassansa kuma sun kakkarye, sun fāɗi a cikin dukan magudanan ruwa na ƙasa. Dukan al’umman duniya suka fito daga ƙarƙashin inuwarsa suka bar shi. 13Dukan tsuntsaye sararin sama suka zauna a itacen da ya fāɗi, dukan namun jeji kuma suna cikin rassansa. 14Saboda haka ba wani daga cikin itatuwan da suke kusa da ruwan da zai taɓa yin fariyar tsawonsa, har kawunansu su kai cikin gizagizai. Ba wani daga cikin itatuwan da ya sha ruwa sosai da zai taɓa yi wannan tsayi; duk an bashe su ga mutuwa, zuwa can ƙasa, a cikin matattu, tare da waɗanda suka gangara zuwa rami.

15“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a ranar da aka yi ƙasa da shi zuwa kabari
Da Ibraniyanci Sheol; haka ma yake a ayoyi 16 da 17.
na rufe zurfafa maɓulɓulai da makoki dominsa; na janye rafuffukansa, aka kuma hana yalwan ruwansa. Saboda shi na rufe Lebanon da baƙin ciki, dukan itatuwan kurmi suka bushe.
16Na sa al’ummai suka yi rawar jiki da jin ƙarar fāɗuwarsa sa’ad da na yi ƙasa da shi zuwa kabari tare da waɗanda suka gangara rami. Sai dukan itatuwan Eden, zaɓaɓɓu da kuma mafi kyau na Lebanon, dukan itatuwan da aka yi musu banruwa, sun ta’azantu a ƙarƙashin ƙasa. 17Waɗanda suka zauna a inuwarsa, dukan masu tarayyarsa a cikin al’ummai, su ma sun gangara zuwa kabari tare da shi, sun haɗu da waɗanda aka kashe da takobi.

18“ ‘Da wa cikin itatuwan Eden za a kwatanta da kai cikin girma da daraja? Duk da haka kai ma, za a yi ƙasa da kai tare da itatuwan Eden zuwa ƙarƙashin ƙasa; za ka kwanta a cikin marasa kaciya, tare da waɗanda aka kashe da takobi.

“ ‘Fir’auna ke nan da dukan jama’arsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”
Copyright information for HauSRK