‏ Genesis 25:12-16

’Ya’yan Ishmayel maza

(1 Tarihi 1.28-31)

12Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.

13Ga jerin sunayen’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu,

Nebayiwot ɗan farin Ishmayel,
Kedar, Adbeyel, Mibsam,
14Mishma, Duma, Massa,
15Hadad, Tema, Yetur,
Nafish da Kedema.

16Waɗannan su ne’ya’yan Ishmayel maza, waɗanda kuma suke sunayen kabilu goma sha biyu masu mulki bisa ga wuraren zamansu da sansaninsu.
Copyright information for HauSRK