Genesis 49
Yaƙub ya albarkaci’ya’yansa maza
1Sai Yaƙub ya kira’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa. 2“Ku tattaru, ku saurara,’ya’yan Yaƙub maza;ku saurari mahaifinku, Isra’ila.
3“Ruben, kai ne ɗan farina,
ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina,
mafi matsayi, kuma mafi iko.
4Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba,
gama ka hau gadon mahaifinka
ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.
5“Simeyon da Lawi’yan’uwa ne,
takubansu makamai ne na tā da hankali.
6Ba zan shiga shawararsu ba,
ba zan shiga taronsu ba,
gama sun kashe maza cikin fushinsu
cikin ganin dama suka kashe bijimai.
7La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai,
hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai!
Zan warwatsa su cikin Yaƙub
in kuma daidaita su cikin Isra’ila.
8“Yahuda, ▼
▼Yahuda ya yi kamar ya fito daga Ibraniyanci na yabo ne.
’yan’uwanka za su yabe ka;hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka,
’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.
9Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda,
ka dawo daga farauta, ɗana.
Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe,
kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?
10Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba,
ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba,
sai ya zo ga wanda yake mai shi ▼
▼Ko kuwa sai Shilo ya zo; ko kuwa sai ya zo ga girma ya dace.
.Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.
11Zai daure jakinsa a kuringa,
aholakinsa a rassa mafi kyau;
zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi
rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.
12Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi,
haƙorarsa farare kamar madara. ▼
▼Ko kuwa zai zama marar walƙiya daga ruwan inabi, haƙorarsa farare daga madara
13“Zebulun zai zauna a bakin teku,
yă zama tasar jiragen ruwa;
iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.
14“Issakar doki ▼
▼Ko kuwa mai ƙarfi
mai ƙarfi,kwance tsakanin buhunan sirdi. ▼
▼Ko kuwa sansanin wuta
15Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau
da kuma daɗin da ƙasarsa take,
zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi
yă miƙa kai ga aikin dole.
16“Dan ▼
▼Dan a nan yana nufin yakan tanada adalci.
zai tanada adalci wa mutanensakamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.
17Dan zai zama maciji a gefen hanya,
kububuwa a bakin hanya,
da take saran ɗiɗɗigen doki
domin mahayinsa yă fāɗi da baya.
18“Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
19“Masu fashi za su fāɗa wa Gad, ▼
▼Gad na iya nufin fāɗawa da kuma ƙungiyar mahara.
amma zai runtume su.
20“Abincin Asher zai zama a wadace,
zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.
21“Naftali sakakkiyar barewa ce
da take haihuwar kyawawan’ya’ya. ▼
▼Ko kuwa yakan faɗa kyawawan kalmomi
22“Yusuf kuringa ce mai ba da amfani.
Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi
wadda rassanta na hawan bango. ▼
▼Ko kuwa Yusuf aholakin jeji ne, aholakin jeji kusa da rafi, jakin jeji a tudun mai kunyoyi
23Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa;
suka harbe shi babu tausayi.
24Amma bakansa yana nan daram
hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa ▼
▼Ko kuwa mahara za su fāɗa, za su harba, za su rage, za su tsaya
saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub,
saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,
25saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka,
saboda Maɗaukaki, ▼
▼Da Ibraniyanci Shaddai
wanda yake albarkace kada albarkar sama da take bisa
albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa
albarkun mama da kuma mahaifa.
26Albarkun mahaifi suna da girma fiye
da albarkun daɗaɗɗun duwatsu
fiye ▼
▼Ko kuwa kakana, mai girma kamar
da yalwar madawwaman tuddai.Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf,
a goshin ɗan sarki a cikin ▼
▼Ko kuwa wanda aka raba da
’yan’uwansa.27“Benyamin kyarkeci ne mai kisa;
da safe yakan cinye abin da ya farauto
da yamma yakan raba ganima.”
28Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.
Mutuwar Yaƙub
29Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti, 30kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti. 31A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu. 32Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.” ▼▼Ko kuwa ’ya’ya mazan Het
33Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.
Copyright information for
HauSRK