Isaiah 12
Waƙoƙin yabo
1A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji.Ko da yake a dā ka yi fushi da ni,
amma yanzu ka daina fushi da ni
ka kuwa ta’azantar da ni.
2Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;
zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.
Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;
ya zama mai cetona.”
3Da farin ciki zan ɗebo ruwa
daga rijiyoyin ceto.
4A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;
a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,
a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.
5Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;
bari a sanar da wannan ga dukan duniya.
6Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona,
gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”
Copyright information for
HauSRK