Isaiah 16
1Ku aiko da raguna a matsayin harajiga mai mulkin ƙasar,
daga Sela a hamada,
zuwa dutsen Diyar Sihiyona.
2Kamar tsuntsaye masu firiya
da aka kora daga sheƙa,
haka matan Mowab suke
a kogunan Arnon.
3“Ku ba mu shawara,
ku yanke shawara.
Ku mai da inuwarku kamar dare,
a tsakar rana.
Ku ɓoye masu gudun hijira,
kada ku bashe masu neman mafaka.
4Ku bar Mowabawa masu gudun hijira su zauna tare da ku;
ku zama mafakarsu daga mai neman hallaka su.”
Mai danniya zai zo ga ƙarshe
hallaka kuma za tă daina;
masu lalatar da ƙasa za su kare
5Da ƙauna za a kafa kursiyi;
da aminci mutum zai zauna a kansa,
wani daga gidan ▼
▼Da Ibraniyanci tenti
Dawuda,wani wanda ta shari’antawa yakan nuna gaskiya
ya hanzarta yin adalci.
6Mun ji fariyar Mowab,
mun ji yawan fariyarta da girmankanta,
fariyarta da reninta,
amma taƙamarsu ta banza ce.
7Saboda haka Mowabawa za su yi kuka mai zafi,
za su yi kuka mai zafi tare saboda Mowab.
Ku yi makoki ku kuma yi baƙin ciki
saboda ƙosai da kuka riƙa ci a Kir Hareset.
8Gonakin Heshbon sun bushe,
inabin Sibma ma haka.
Masu mulkin al’ummai
sun tattake inabi mafi kyau,
waɗanda suka taɓa yaɗuwa zuwa Yazer
suka bazu ta wajen hamada.
Tohonsu sun buɗu
suka kai har teku.
9Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka,
saboda inabin Sibma.
Ya Heshbon, ya Eleyale,
na cika ku da hawaye!
Sowa ta murna a kanku saboda’ya’yan itatuwanku da suka nuna
da kuma girbinku sun ɓace.
10An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu’ya’ya;
babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi;
babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi,
gama na kawo ƙarshen yin sowa.
11Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya,
na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.
12Sa’ad Mowab ta bayyana a masujadar bisa tudu,
tana gajiyar da kanta ne kawai;
sa’ad da ta tafi wurin tsafinta don tă yi addu’a,
babu wani amfani.
13Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya riga ya yi game da Mowab. 14Amma yanzu Ubangiji ya ce, “Cikin shekara uku, kamar yadda bawan da aka bautar da shi bisa ga yarjejjeniya zai lissafta, haka za a mai da daraja da kuma dukan yawan mutanen Mowab abin reni, daga ɗumbun mutanenta,’yan kaɗan ne kaɗai za su ragu, za su kuma zama marasa ƙarfi.”
Copyright information for
HauSRK