‏ Isaiah 31

Kaiton waɗanda suke dogara ga Masar

1Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako,
waɗanda suke dogara ga dawakai,
waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu
da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu,
amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila,
ko ya nemi taimako daga Ubangiji.
2Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa;
ba ya janye kalmominsa.
Zai yi gāba da gidan mugu,
gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.
3Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba;
dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba.
Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa,
shi da yake taimako zai yi tuntuɓe
shi da aka taimaka zai fāɗi;
dukansu biyu za su hallaka tare.

4Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini, “Kamar yadda zaki kan yi ruri
babban zaki a kan abin da ya yi farauta,
kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyaya
sun taru wuri ɗaya a kansa,
ba zai jijjigu ta wurin ihunsu ba
ko ya damu da kiraye-kirayensu,
ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai sauko
don yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.
5Kamar tsuntsaye masu shawagi a sama
haka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima;
zai kāre ta ya kuma fanshe ta,
zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”

6Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa. 7Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi. 8“Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba;
takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye.
Za su gudu daga takobi
za a kuma sa samarinsu aikin dole.
9Kagararsu za tă fāɗi saboda razana;
da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,”
in ji Ubangiji,
wanda wutarsa tana a Sihiyona,
wanda matoyarsa tana a Urushalima.
Copyright information for HauSRK