‏ Isaiah 37:14-20

Addu’ar Hezekiya

(2 Sarakuna 19.14-19)

14Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji. 15Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, 16“Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya. 17Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.

18“Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango. 19Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa. 20Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.”
Copyright information for HauSRK