‏ Jeremiah 40:7-9

An yi wa Gedaliya kisan gilla

7Sa’ad da dukan shugabannin hafsoshin tare da mutanen da suke a karkara suka ji cewa sarkin Babilon ya naɗa Gedaliya ɗan Ahikam gwamna a kan ƙasar ya kuma sa shi ya lura da maza, mata da’ya’yan da suke mafi talauci a ƙasar da waɗanda ba a kwashe zuwa zaman bauta a Babilon ba, 8sai suka zo wurin Gedaliya a Mizfa, Ishmayel ɗan Netaniya, Yohanan da Yonatan’ya’yan Kareya, da Serahiya ɗan Tanhumet maza,’ya’yan Efai maza, mutumin Netofa, da Yezaniya
Da Ibraniyanci Yezaniya, wani suna na Ya’azaniya
ɗan mutumin Ma’aka da mutanensu.
9Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, ya yi rantsuwa don yă tabbatar musu da mutanensu. Ya ce, “Kada ku ji tsoron bauta wa Babiloniyawa.
Ko kuwa Kaldiyawa; haka ma a aya 10
Ku zauna a ƙasar ku bauta wa sarkin Babilon, zai kuma yi muku amfani.
Copyright information for HauSRK