‏ Jeremiah 48

Saƙo game da Mowab

1Game da Mowab.

Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, “Kaito ga Nebo, gama za tă lalace.
Kiriyatayim za su kunyata a kuma kame ta;
katagar
Ko kuwa / Misgab
za tă sha kunya ta kuma wargaje.
2Ba za a ƙara yabi Mowab ba;
a Heshbon
Da Ibraniyanci na Heshbon ya yi kamar Ibraniyanci na maƙarƙashiya.
mutane za su shirya mata maƙarƙashiya.
‘Zo, mu tafi mu kawo ƙarshe ga wannan al’umma.’
Ke kuma, ya Madmen
Sunan garin Mowab nan Madmen ya yi kamar Ibraniyanci na yi shiru.
za ki yi shiru;
takobi zai fafare ki.
3Saurari kuka daga Horonayim,
kukan risɓewa mai girma da hallaka.
4Za a karye Mowab;
ƙanananta za su yi kuka.
5Sun haura hanyar zuwa Luhit,
suna kuka mai zafi yayinda suke tafiya;
a hanyar da ta gangara zuwa Horonayim
suna kuka a kan hallakar da aka ji.
6Ku gudu! Ku gudu don tserar da ranku;
ku zama kamar kurmi
Ko kuwa kamar Arower
a hamada.
7Da yake kun dogara ga ayyukanku da arzikinku,
ku ma za a kwashe ku bayi,
Kemosh zai tafi bauta,
tare da firistocinsa da fadawansa.
8Mai hallakarwa zai aukar wa kowane gari,
kuma ba wani garin da zai kuɓuta.
Kwari zai lalace
tudu kuma ya hallaka,
domin Ubangiji ya faɗa.
9Ku sa gishiri a kan Mowab,
gama za tă zama kango;
Ko kuwa Ku ba wa Mowab fikafikai, don tă tashi tă tafi

garuruwanta za su zama kufai,
ba mazauna a cikinsu.

10“La’ananne ne shi wanda yake sake a yin aikin Ubangiji!
La’ananne ne wanda ya janye takobinsa daga zub da jini!

11“Mowab ta kasance cikin kwanciyar rai tun ƙuruciyarta,
kamar ruwan inabin da aka bari lis,
ba a juya daga tulu zuwa wani tulu ba
ba tă tafi bauta ba.
Saboda haka tana da ɗanɗanonta,
kuma ƙanshinta bai canja ba.
12Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji,
“sa’ad da zan aika da mutanen da za su tuntsurar da tuluna,
su kuma zubar da ita waje.
Za su bar tulunan ba kome a ciki
su kuma farfashe tulunanta.
13Sa’an nan Mowab za tă ji kunyar Kemosh,
yadda gidan Isra’ila ya ji kunya
sa’ad da suka dogara ga Betel.

14“Yaya za ku ce, ‘Mu jarumawa ne,
mutane masu ƙarfi a yaƙi?’
15Mowab za tă hallaka a kuma kai wa garuruwanta hari;
samarinta kyawawa za su gangara cikin mayanka,”
in ji Sarki, wanda sunansa Ubangiji Maɗaukaki ne.
16“Fāɗuwar Mowab ta yi kusa;
bala’inta zai auku nan da nan.
17Yi kuka saboda ita, dukanku mazaunan kewayenta,
duk waɗanda suka san shahararta;
ku ce, ‘Dubi yadda sandan sarauta mai iko ya karye,
dubi yadda sanda mai daraja ya karye!’

18“Sauko daga darajarku
ku zauna a busasshiyar ƙasa,
Ya mazaunan Diyar Dibon,
gama shi mai hallaka Mowab
zai haura a kanku
zai kuma lalace biranenku masu kagarai.
19Ku tsaya a bakin hanya ku duba,
ku da kuke zama a Arower.
Ku tambayi mutumin da yake gudu da macen da take tserewa,
tambaye su, ‘Me ya faru?’
20An kunyata Mowab, gama ta wargaje.
Ku yi kuka ku kuma tā da murya!
Ku yi shela kusa da Arnon
cewa an hallaka Mowab.
21Hukunci ya zo wa tudu,
zuwa Holon, Yahza da Mefa’at,
22zuwa Dibon, Nebo da Bet-Dibilatayim,
23zuwa Kiriyatayim, Bet-Gamul da Bet-Meyon,
24zuwa Keriyot da Bozra
zuwa dukan garuruwan Mowab, nesa da kusa.
25An karye ƙahon Mowab;
an karye hannunta,”
in ji Ubangiji.

26“Ku bugar da ita
domin ta tayar wa Ubangiji.
Bari Mowab tă yi ta birgima a cikin amanta;
bari tă zama abin dariya.
27Isra’ila ma bai zama abin dariya a gare ki ba?
Ba a kama shi cikin ɓarayi,
har kaɗa kai na ba’a kike yi
a duka sa’ad da kike magana game da shi?
28Ku bar garuruwanku ku zauna a cikin duwatsu,
ku da kuke zama a Mowab.
Ku zama kamar kurciyar da take sheƙarta
a bakin kogo.

29“Mun ji labarin girman kan Mowab
mun ji alfarma girmankanta da kumburinta
girmankanta da fariyarta
da renin zuciyarta.
30Na san alfarmanta amma a banza ne,” in ji Ubangiji,
“kuma taƙamarta ba ya cimma kome.
31Saboda haka zan yi kuka a kan Mowab
gama dukan Mowab zan yi kuka,
Zan yi gurnani don mutanen Kir Hareset.
32Zan yi kuka saboda kai, yadda Yazer ya yi kuka
Ya kuringar Sibma.
Rassanki sun kai har teku;
sun kai har tekun Yazer.
Mai hallakarwa ya fāɗo
a kan’ya’yan itatuwanku da kuma inabinku da suka nuna.
33Farin ciki da murna su ɓace
daga lambunan itatuwa da kuma gonakin Mowab.
Na dakatar da malalar ruwan inabi daga wurin matsi;
ba wanda zai matse su da ihun farin ciki.
Ko da yake akwai sowa
sowar ba ta farin ciki ba ce.

34“Muryar kukansu na tashi
daga Heshbon zuwa Eleyale da Yahaz,
daga Zowar har zuwa Horonayim da Eglat Shelishiya,
gama har ruwan Nimrim ma sun bushe.
35A Mowab zan kawo ƙarshen
waɗanda suke miƙa hadayu a masujadan kan tudu
suna kuma ƙone turare ga allolinsu,”
in ji Ubangiji.
36“Saboda haka zuciyata na makoki don Mowab kamar busa;
tana makoki kamar busa saboda mutanen Kir Hareset.
Arzikin da suka samu ta ƙare.
37An aske kowane kai
aka kuma yanke kowane gemu
aka kuma sa wa kowane kwankwaso rigar makoki.
38A kan dukan rufi a Mowab
da kuma a dandalin jama’a
babu wani abu sai kuka
gama na karye Mowab
kamar tulun da babu mai so,”
in ji Ubangiji.
39“Duba yadda aka ragargazar ta ita! Duba yadda suke kuka!
Duba yadda Mowab ta juya bayanta da kunya!
Mowab ta zama abin ba’a
abin tsoro ga dukan waɗanda suke kewaye da ita.”

40Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ga shi! Gaggafa tana firiya zuwa ƙasa,
tana shimfiɗa fikafikanta a kan Mowab.
41Za a ci Keriyot
Ko kuwa Birane

a kuma kame kagarai.
A wannan rana zukatan jarumawan Mowab
za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.
42Za a hallakar da Mowab a matsayin al’umma
domin ta tayar wa Ubangiji.
43Razana da rami da tarko suna jiranku,
Ya mutanen Mowab,”
in ji Ubangiji.
44“Duk wanda ya gudu daga razana
zai fāɗa cikin rami,
duk wanda ya haura daga rami
zai fāɗa cikin tarko;
gama zan kawo wa Mowab
shekarar hukuncinta,”
in ji Ubangiji.

45“A ƙarƙashin Heshbon
masu gudun hijira suna tsaye ba mai taimako,
gama wuta ta mutu daga Heshbon,
harshen wuta daga tsakiyar Sihon;
ta ƙone goshin Mowab,
ƙoƙon kai na’yan tayarwa masu surutu.
46Kaitonki, ya Mowab!
Mutanen Kemosh sun hallaka;
an kai’ya’yanki maza daurin talala
’ya’yanki mata zaman bauta.

47“Duk da haka zan maido da wadatar Mowab
a kwanaki masu zuwa,”
in ji Ubangiji.

A nan hukuncin Mowab ya ƙare.
Copyright information for HauSRK