Job 10
1“Na gaji da rayuwa;saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi
yadda raina yake jin ba daɗi.
2Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni,
amma ka gaya mini laifin da na yi maka.
3Kana jin daɗin ba ni wahala,
don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka,
yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?
4Idanunka irin na mutum ne?
Kana gani yadda mutum yake gani ne?
5Kwanakinka kamar na mutane ne,
ko shekarunka kamar na mutane ne
6da za ka neme ni da laifi
ka hukunta ni?
7Ko da yake ka san ba ni da laifi,
kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.
8“Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni.
Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?
9Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu.
Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?
10Ba kai ka zuba ni kamar madara ba,
na daskare kamar cuku.
11Ka rufe ni da tsoka da fata,
ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?
12Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri,
kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.
13“Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka,
na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.
14In na yi zunubi kana kallo na
kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.
15Idan ina da laifi, kaitona!
Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba,
gama kunya ta ishe ni
duk ɓacin rai ya ishe ni.
16In na ɗaga kaina, za ka neme ni kamar zaki
ka sāke nuna al’ajabin ikonka a kaina.
17Kana sāke kawo sababbin waɗanda za su ba da shaida a kaina
kana ƙara haushinka a kaina;
kana ƙara kawo mini hari.
18“Me ya sa ka fito da ni daga cikin uwata?
Da ma na mutu kafin a haife ni.
19Da ma ba a halicce ni ba,
da na mutu tun daga cikin cikin uwata na wuce zuwa kabari!
20’Yan kwanakina ba su kusa ƙarewa ba ne?
Ka rabu da ni don in ɗan samu sukuni na ɗan lokaci
21kafin in koma inda na fito,
ƙasa mai duhu da inuwa sosai,
22zuwa ƙasa mai duhun gaske,
da inuwa da hargitsi,
inda haske yake kamar duhu.”
Copyright information for
HauSRK