Job 13
1“Idanuna sun ga waɗannan duka,kunnuwana sun ji sun kuma gane.
2Abin da kuka sani, ni ma na sani;
ba ku fi ni ba.
3Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki,
in kai kukana wurin Allah kai tsaye.
4Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi;
ku likitocin wofi ne, dukanku!
5In da za ku yi shiru gaba ɗaya!
Zai zama muku hikima.
6Ku ji gardamata yanzu;
ku ji roƙon da zai fito daga bakina.
7Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah?
Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?
8Ko za ku nuna masa sonkai?
Ko za ku yi gardama a madadinsa?
9In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi?
Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?
10Ba shakka zai kwaɓe ku
in kun nuna sonkai a ɓoye.
11Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro?
Tsoronsa ba zai auka muku ba?
12Duk surutanku kamar toka suke;
kāriyarku na yimɓu ne.
13“Ku yi shiru zan yi magana;
sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.
14Don me na sa kaina cikin hatsari
na yi kasada da raina?
15Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance;
ba shakka zan kāre kaina a gabansa
16lalle wannan zai kawo mini kuɓuta
gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa!
17Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa;
bari kunnuwanku su ji abin da zan ce.
18Yanzu da na shirya ƙarata,
na san za a ce ba ni da laifi.
19Ko wani zai ce ga laifin da na yi?
In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.
20“Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah,
ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba;
21Ka janye hannunka nesa da ni,
ka daina ba ni tsoro da bantsoronka.
22Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa,
ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini.
23Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne?
Ka nuna mini laifina da zunubina.
24Don me ka ɓoye mini fuskarka;
ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka?
25Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa?
Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?
26Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni;
ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.
27Ka daure ƙafafuna da sarƙa;
kana kallon duk inda na taka
ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.
28“Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu,
kamar rigar da asu ya cinye.
Copyright information for
HauSRK