Job 15
Elifaz
1Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa, 2“Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gadoko yă cika cikinsa da iskar gabas?
3Ko zai yi gardama da maganganun wofi
maganganu marasa amfani?
4Amma ka ma rena Allah
ka hana a yi addu’a gare shi.
5Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce;
kana magana kamar mai wayo.
6Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba;
maganar bakinka za tă juya a kanka.
7“Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa?
Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai?
8Kana sauraron shawarar Allah?
Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?
9Me ka sani da ba mu sani ba?
Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi?
10Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu
mutanen da sun girme babanka.
11Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba.
Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?
12Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka,
kuma don me idanunka suke haske,
13har kake fushi da Allah
kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?
14“Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki,
ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci?
15In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba,
in har sammai ba su da tsarki a idonsa,
16mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa,
wanda yake shan mugunta kamar ruwa!
17“Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani;
bari in gaya maka abin da na gani,
18abin da masu hikima suka ce,
ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba
19(waɗanda su ne masu ƙasar
kafin baƙi su shigo ƙasar).
20Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala,
wahala kaɗai zai yi ta sha.
21Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa
’yan fashi za su kai masa hari.
22Yana jin tsoron duhu
domin za a kashe shi da takobi.
23Yana ta yawo, abinci don ungulaye; ▼
▼Ko kuwa yawo, neman abinci
ya san ranar duhu tana kusa.
24Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi,
kamar sarkin da yake shirin yaƙi,
25domin ya nuna wa Allah yatsa
ya rena Allah Maɗaukaki,
26ya tasar masa da faɗa
da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.
27“Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu
kuma yana da tsoka ko’ina,
28zai yi gādon garuruwan da suka lalace,
da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki,
gidajen da sun zama tarkace.
29Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba,
abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba.
30Ba zai tsere wa duhu ba;
wuta za tă ƙona rassansa,
kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi.
31Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani
domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.
32Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka,
kuma rassansa ba za su ba da amfani ba.
33Zai zama kamar itacen inabi wanda’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna,
kamar itacen zaitun zai zubar da furensa.
34Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da’ya’ya,
wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci.
35Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta;
cikinsu yana cike da ruɗami.”
Copyright information for
HauSRK