Job 18
Bildad
1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, 2“Yaushe za ka gama maganganun nan?Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.
3Don me muke kamar shanu a wurinka,
ka ɗauke mu mutanen wofi?
4Kai da ka yayyage kanka don haushi,
za a yashe duniya saboda kai ne?
Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?
5“An kashe fitilar mugu;
harshen wutarsa ya daina ci.
6Wutar cikin tentinsa ta zama duhu;
fitilar da take kusa da shi ta mutu.
7Ƙarfin takawarsa ya ragu;
dabararsa ta ja fāɗuwarsa.
8Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga,
yana ta yawo a cikin ragar.
9Tarko ya kama ɗiɗɗigensa;
tarko ya riƙe shi kam.
10An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa;
an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.
11Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe
yana bin shi duk inda ya je.
12Masifa tana jiransa;
bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.
13Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa;
ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.
14An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa
aka sa shi tsoro sosai.
15Wuta ta cinye tentinsa;
farar wuta ta rufe wurin da yake zama.
16Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa
rassansa sun mutu a sama.
17An manta da shi a duniya;
ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
18An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu,
an kore shi daga duniya.
19Ba shi da’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa,
ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.
20Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi;
tsoro ya kama mutanen gabas.
21Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake,
haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”
Copyright information for
HauSRK