Job 19
Ayuba
1Sai Ayuba ya amsa, 2“Har yaushe za ku yi ta ba ni azabaku kuma murƙushe ni da maganganunku?
3Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni,
kuna kai mini hari na rashin kunya.
4In gaskiya ne na yi laifi,
kuskurena ya rage nawa.
5In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina
kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,
6sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba
ya kewaye ni da ragarsa.
7“Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba;
ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.
8Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba;
ya rufe hanyata da duhu.
9Ya cire darajar da nake da ita,
ya kuma cire rawani daga kaina.
10Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare;
ya tuge begen da nake da shi kamar itace.
11Yana jin haushina
ya lissafta ni cikin maƙiyansa.
12Rundunarsa ta zo da ƙarfi;
suka kafa sansani kewaye da ni,
suka zagaye tentina.
13“Ya raba ni da’yan’uwana maza;
abokaina sun zama baƙi gare ni.
14Dangina sun tafi;
abokaina na kurkusa sun manta da ni.
15Waɗanda sukan ziyarce ni,
da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.
16Na kira bawana, amma bai amsa ba,
ko da yake na roƙe shi da bakina.
17Numfashina yana ɓata wa matata rai;
’yan’uwana sun ƙi ni.
18Har’yan yara suna rena ni;
in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.
19Duk abokaina sun yashe ni;
waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.
20Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi,
da ƙyar na tsira.
21“Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina,
gama hannun Allah ya sauko a kaina.
22Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi?
Ba ku gaji da yagar fatata ba?
23“Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna,
da an rubuta su a littafi,
24a rubuta su da ƙarfe a kan dutse
don su dawwama har abada!
25Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai,
kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.
26Kuma bayan an hallaka fatata,
duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.
27Zan gan shi da kaina
da idanuna, Ni, ba wani ba ne.
Zuciyata ta cika da wannan tunani!
28“In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini,
tun da shi ne tushen damuwa,’
29sai ku ma ku ji tsoron takobin;
gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi,
sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”
Copyright information for
HauSRK