‏ Job 20

Zofar

1Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa, 2“Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa
domin abin ya dame ni sosai.
3Na ji wani zargin da ka yi mini na reni,
kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa.

4“Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni,
tun da aka sa mutum cikin duniya,
5mugun mutum bai taɓa daɗewa ba,
farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.
6Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama,
kansa kuma yana taɓa gizagizai.
7Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa;
waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’
8Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba
zai ɓace kamar wahayi da dare.
9Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba;
wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba.
10Dole’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata;
dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa.
11Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa
zai kwantar da shi a cikin ƙura.

12“Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa
kuma yana ɓoye ta a harshensa,
13ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba,
yana kuma ajiye ta a bakinsa,
14duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa;
zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.
15Zai haras da dukiyar da ya haɗiye;
Allah zai sa cikinsa yă haras da su.
16Zai sha dafin maciji;
sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.
17Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka
masu kwarara da zuma da madara ba.
18Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu,
ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.
19Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala;
ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.

20“Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba,
dukiyarsa ba za tă cece shi ba.
21Ba abin da ya ragu da zai ɗauka;
arzikinsa ba zai dawwama ba.
22Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa;
ƙunci mai ƙarfi zai zo masa.
23Lokacin da ya cika cikinsa,
Allah zai zuba fushinsa a kansa,
zai daddaka shi.
24Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe,
kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi.
25Zai zāre ta daga bayansa,
tsinin zai fita daga hantarsa;
tsoro zai cika shi;
26duhu kawai yake jiran dukiyarsa.
Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi
ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa.
27Sammai za su fallasa laifinsa;
duniya za tă yi gāba da shi.
28Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa,
ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.
29Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan,
gādon da Allah ya ba shi ke nan.”
Copyright information for HauSRK