‏ Job 21

Ayuba

1Sai Ayuba ya amsa, 2“Ku saurare ni da kyau;
bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni.
3Ku ba ni zarafi in yi magana,
bayan na gama sai ku yi ba’arku.

4“A wurin mutum ne na kawo kukana?
Don me ba zan kāsa haƙuri ba?
5Ku dube ni, ku kuma yi mamaki;
ku rufe bakina da hannunku.
6Lokacin da na yi tunanin wannan,
sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa.
7Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa,
suna kuma ƙaruwa da iko?
8Suna ganin’ya’yansu suna girma,
suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.
9Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba.
Kuma Allah ba ya ba su horo.
10Shanunsu ba sa fasa haihuwa;
suna haihuwa ba sa yin ɓari.
11Suna aika’ya’yansu kamar garke;
’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.
12Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya;
suna jin daɗin busar sarewa.
13Suna yin rayuwarsu cikin arziki
kuma su mutu cikin salama.
14Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’
Ba ma so mu san hanyoyinka.
15Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa?
Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?
16Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba
saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.

17“Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa?
Sau nawa bala’i yake auka masa,
ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?
18Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska,
ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?
19An ce ‘Allah yana tara wa’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’
Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!
20Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka;
bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.
21Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya
sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?

22“Wani zai iya koya wa Allah ilimi
tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?
23Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi
da kwanciyar hankali,
24jikinsa ɓulɓul,
ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.
25Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai,
bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.
26Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa,
kuma tsutsotsi za su cinye su.

27“Na san duk abin da kuke tunani,
yadda za ku saɓa mini.
28Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan,
tenti wurin da mugaye suke zama?’
29Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba?
Ba ku kula da labaransu,
30cewa an kāre mugu daga ranar bala’i,
an kāre shi daga ranar fushi?
31Wane ne yake gaya masa abin da ya yi?
Wane ne yake rama abin da ya yi?
32Za a bizne shi a kabari,
a kuma yi tsaron kabarinsa.
33Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali;
dukan jama’a suna binsa,
da yawa kuma suna gabansa.

34“Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya
da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!”
Copyright information for HauSRK