Job 22
Elifaz
1Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa, 2“Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah?Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?
3Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne?
Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?
4“Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka
ya kuma bari haka yă same ka?
5Ba muguntarka ce ta yi yawa ba?
Ba zunubanka ne ba iyaka ba?
6Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili;
ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.
7Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba
kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.
8Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa,
mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.
9Ka kori gwauraye hannu wofi,
ka kuma karya ƙarfin marayu.
10Shi ya sa kake kewaye da tarkuna,
shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.
11An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani,
shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.
12“Ba Allah ne a can sama ba?
Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!
13Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani?
A cikin duhu ne yake shari’a?
14Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu
lokacin da yake takawa a cikin sammai.’
15Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar
da mugayen mutane suka bi?
16An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika,
ruwa ya share tushensu.
17Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu!
Me Maɗaukaki zai yi mana?’
18Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau,
saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.
19“Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi;
marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa,
20‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu,
wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’
21“Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa;
ta haka ne arziki zai zo maka.
22Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa
kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.
23In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke.
In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.
24Ka jefar da zinariyarka a ƙasa,
ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,
25sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka,
zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.
26Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki
daga wurin Maɗaukaki,
ku kuma ɗaga idanunku ga Allah
27Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka,
kuma za ka cika alkawuranka.
28Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki,
haske kuma zai haskaka hanyarka.
29Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’
Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.
30Zai ceci wanda ma yake mai laifi,
wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.”
Copyright information for
HauSRK