Job 23
Ayuba
1Sa’an nan Ayuba ya amsa, 2“Ko a yau, ina kuka mai zafi;hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi.
3Da a ce na san inda zan same shi;
da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama!
4Zan kai damuwata wurinsa
in yi gardama da shi.
5Zan nemi in san abin da zai ce mini,
in kuma auna abin da zai ce mini.
6Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma?
Babu, ba zai zarge ni da laifi ba.
7Mai adalci ne zai kawo ƙara a wurinsa,
kuma zan samu kuɓuta daga wurin mai shari’an nan har abada.
8“Amma in na je gabas, ba ya wurin;
in na je yamma, ba zan same shi ba.
9Sa’ad da yake aiki a arewa, ba ni ganinsa;
sa’ad da ya juya zuwa kudu, ba na ganinsa.
10Amma ya san hanyar da nake bi;
sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya.
11Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa;
na bi hanyarsa ba tare da na juya ba.
12Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba;
na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe.
13“Amma ya tsaya shi kaɗai, kuma wa ya isa yă ja da shi?
Yana yin abin da yake so.
14Yana yi mini abin da ya shirya yă yi mini,
kuma yana da sauran irinsu a ajiye.
15Shi ya sa na tsorata a gabansa;
sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa.
16Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi;
Maɗaukaki ya tsorata ni.
17Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba,
duhun da ya rufe mini fuska.
Copyright information for
HauSRK