‏ Job 25

Bildad

1Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, 2“Mulki na Allah ne, dole a ji tsoronsa;
yana tafiyar da kome yadda ya kamata a cikin sama.
3Za a iya ƙirga rundunarsa?
A kan wane ne ba ya haska haskensa?
4Ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?
Ta yaya mutumin da mace ta haifa zai zama mai tsarki?
5In har wata da taurari
ba su da tsarki a idanunsa,
6mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai.
Me mutum ya daɗa a gaban Allah!”
Copyright information for HauSRK