‏ Job 26

Ayuba

1Sai Ayuba ya amsa, 2“Yadda ka taimaki marar ƙarfi!
Yadda ka ceci marar ƙarfi!
3Ka ba marar hikima shawara!
Ka nuna kana da ilimi sosai.
4Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu?
Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?

5“Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye
da dukan mazauna cikin ruwaye.
6Mutuwa tsirara take a gaban Allah;
haka kuma hallaka take a buɗe.
7Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari;
ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.
8Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,
duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.
9Ya rufe fuskar wata,
ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,
10ya zāna iyakar fuskar ruwa
a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.
11Madogaran sama sun girgiza,
saboda tsawatawarsa.
12Da ikonsa ya kwantar da teku;
da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.
13Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau
da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.
14Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa.
Kaɗan kawai muke ji game da shi!
Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”
Copyright information for HauSRK