‏ Job 27

1Ayuba kuwa ya ci gaba da magana, 2“Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata,
Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
3Muddin ina da rai a cikina
kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
4bakina ba zai faɗi mugun abu ba,
harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.
5Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba;
har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.
6Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba;
lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.

7“Bari maƙiyana su zama kamar mugaye,
masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci.
8Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi,
lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?
9Ko Allah yana sauraron kukansa
lokacin da ƙunci ya auko masa?
10Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki?
Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?

11“Zan koya muku game da ikon Allah;
ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba.
12Duk kun ga wannan ku da kanku
saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana?

13“Ga abin da mugaye za su samu
gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.
14Kome yawan’ya’yansa, takobi za tă gama da su;
zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba.
15Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su,
kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba.
16Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa,
tufafi kuma kamar tarin ƙasa,
17abin da ya tara masu adalci za su sa
marasa laifi za su raba azurfarsa.
18Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo,
kamar bukkar mai tsaro.
19Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan;
lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.
20Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa;
Da dare iska za tă tafi da shi.
21Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare;
za tă share shi daga wurinsa.
22Za tă murɗe shi ba tausayi,
lokacin da yake guje wa ikon iskar.
23Zai tafa hannu yă yi tsaki
yă kawar da shi daga wurinsa.”
Copyright information for HauSRK