Job 28
1Akwai ramin azurfaakwai kuma wurin da ake tace zinariya.
2Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe,
ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.
3Mutum ya kawo ƙarshen duhu;
yakan bincike zuzzurfar iyaka,
yana neman duwatsu a wuri mafi duhu.
4Nesa da inda mutane suke zama,
yakan huda rami yă yi abin lilo,
a wurin da mutane ba sa bi.
5Cikin ƙasa inda ake samun abinci,
a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;
6akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta,
akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.
7Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba,
ba shahon da ya taɓa ganin ta.
8Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba,
ba zakin da ya taɓa binta.
9Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu,
yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.
10Yana tona rami a cikin duwatsu
idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.
11Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa
yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.
12Amma a ina ne za a iya samun hikima?
Ina fahimta take zama?
13Mutum bai gane muhimmancinta ba,
ba a samunta a ƙasar masu rai.
14Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”;
teku ya ce, “Ba ta wurina.”
15Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta,
ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.
16Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir,
ko sauran duwatsu masu daraja ba.
17Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba,
ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.
18Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya;
farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.
19Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba,
zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.
20“To, daga ina ke nan hikima ta fito?
Ina fahimta take zama?
21An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai,
har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.
22Hallaka da mutuwa suna cewa,
‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’
23Allah ya gane hanyar zuwa wurinta.
Shi ne kaɗai ya san inda take zama,
24Gama yana ganin iyakar duniya
kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.
25Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura,
ya kuma auna ruwaye.
26Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka
da kuma hanya domin walƙiya,
27sai ya dubi hikima ya auna ta;
ya tabbatar da ita, ya gwada ta.
28Ya kuma ce wa mutum,
‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima,
kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”
Copyright information for
HauSRK