‏ Job 29

1Ayuba ya ci gaba da jawabinsa, 2“Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can,
kwanakin da Allah yake lura da ni,
3lokacin da fitilarsa take haske a kaina
na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.
4Kwanakin da nake tasowa,
lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka,
5lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni,
kuma’ya’yana suna kewaye da ni,
6lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa,
duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun.

7“Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna
a bainin jama’a,
8matasan da suka gan ni sukan ja gefe
tsofaffi kuma suka tashi tsaye;
9sarakuna suka yi shiru
suka rufe bakunansu da hannuwansu;
10Muryar manya ta yi tsit
harshensu ya manne a rufin bakunansu.
11Duk wanda ya ji ni ya yaba mini
waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,
12domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako,
da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.
13Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka.
Na faranta wa gwauruwa zuciya.
14Na yafa adalci ya zama suturata;
gaskiya ita ce rigata da rawanina.
15Ni ne idon makafi
kuma ƙafa ga guragu.
16Ni mahaifi ne ga masu bukata;
na tsaya wa baƙo.
17Na karya ƙarfin mugaye
na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.

18“Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana,
kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.
19Jijiyoyina za su kai cikin ruwa,
kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.
20Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau,
bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’

21“Mutane suna mai da hankali su saurare ni,
suna yin shiru don su ji shawarata.
22Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba.
Maganata ta shige su.
23Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama.
Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.
24Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda;
hasken fuskata yana da daraja a gare su.
25Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu;
na zauna kamar sarki a cikin rundunansu;
ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.
Copyright information for HauSRK