Job 30
1“Amma yanzu suna yi mini ba’awaɗanda na girme su,
waɗanda iyayensu maza ba su isa
su zama karnukan kiwon garken tumakina ba.
2Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni,
tun da ba su da sauran kuzari?
3Duk sun rame don rashi da yunwa,
suna yawo a gaigayar ƙasa
a kufai da dare.
4A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi,
jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu.
5An kore su daga cikin mutanensu,
aka yi musu ihu kamar ɓarayi.
6An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma
cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa.
7Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji,
suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya.
8Mutane marasa hankali marasa suna,
an kore su daga ƙasar.
9“Yanzu kuma’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa
na zama abin banza a gare su.
10Suna ƙyamata suna guduna;
suna tofa mini miyau a fuska.
11Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala
sun raba ni da mutuncina.
12A hannun damana’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar;
sun sa tarko a ƙafafuna,
sun yi shirin hallaka ni.
13Sun ɓata mini hanyata;
sun yi nasara cikin hallaka ni,
ba tare da wani ya taimake su ba.
14Suka nufo ni daga kowane gefe;
suka auko mini da dukan ƙarfinsu.
15Tsoro ya rufe ni;
an kawar mini mutuncina kamar da iska,
dukiyata ta watse kamar girgije.
16“Yanzu raina yana ƙarewa;
kwanakin wahala sun kama ni.
17Dare ya huda ƙasusuwana;
ina ta shan azaba ba hutawa.
18A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina;
ya shaƙe ni kamar wuyan rigata.
19Ya jefa ni cikin laka,
na zama ba kome ba sai ƙura da toka.
20“Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba.
Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai.
21Ka dube ni ba tausayi;
Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka.
22Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska;
ka jujjuya ni cikin hadari.
23Na san za ka sauko da ni ga mutuwa
zuwa wurin da kowane mai rai zai je.
24“Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala.
Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa.
25Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba?
Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?
26Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau,
mugun abu ne ya zo;
Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo.
27Zuciyata ba tă daina ƙuna ba;
ina fuskantar kwanakin wahala.
28Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba.
Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako.
29Na zama ɗan’uwan diloli,
na zama abokan mujiyoyi.
30Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa;
jikina yana ƙuna da zazzaɓi.
31Garayata ta zama ta makoki,
sarewata kuma ta zama ta kuka.
Copyright information for
HauSRK