Job 32
Elihu
1Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne. 2Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba. 3Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi. 4Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka. 5Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata. 6Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru,ku kuma kun girme ni;
shi ya sa na ji tsoro
na kāsa gaya muku abin da na sani.
7Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana;
ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’
8Amma ruhun da yake cikin mutum,
numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.
9Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba,
ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.
10“Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni;
ni ma zan gaya muku abin da na sani.
11Na jira sa’ad da kuke magana,
na ji muhawwararku
lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,
12na saurare ku da kyau.
Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi;
ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.
13Kada ku ce, ‘Mun sami hikima;
Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’
14Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba
kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.
15“Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa;
kalmomi sun kāsa musu.
16Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru,
yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa.
17Ni ma zan faɗi nawa;
ni ma zan faɗi abin da na sani.
18Gama ina cike da magana,
kuma ruhun da yake cikina yana iza ni;
19a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba,
kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa.
20Dole in yi magana in sami lafiya;
dole in buɗe baki in ba da amsa.
21Ba zan nuna wa wani sonkai ba,
ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba;
22gama da a ce na iya daɗin baki,
da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni.
Copyright information for
HauSRK