Job 36
1Elihu ya ci gaba, 2“Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan,zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah.
3Daga nesa na sami sanina;
zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne.
4Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne;
mai cikakken sani yana tare da kai.
5“Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane;
shi mai girma ne cikin manufarsa.
6Ba ya barin mugaye da rai
sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu.
7Ba ya fasa duban masu adalci;
yana sa su tare da sarakuna
yana ɗaukaka su har abada.
8Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi,
ƙunci kuma ya daure su,
9yana gaya musu abin da suka yi,
cewa sun yi zunubi da girman kai.
10Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su
su tuba daga muguntarsu.
11In sun yi biyayya suka bauta masa,
za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata
shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya.
12Amma in ba su saurara ba,
za su hallaka da takobi
kuma za su mutu ba ilimi.
13“Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi;
ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa.
14Suna mutuwa tun suna matasa,
cikin ƙazamar rayuwar karuwanci.
15Amma yana kuɓutar da masu wahala;
yana magana da su cikin wahalarsu.
16“Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci,
zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi
zuwa teburinka cike da abincin da kake so.
17Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye;
shari’a da kuma gaskiya sun kama ka.
18Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki;
kada ka bar toshiya ta sa ka juya.
19Dukiyarka
ko dukan yawan ƙoƙarinka
sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci?
20Kada ka yi marmari dare yă yi,
don a fitar da mutane daga gidajensu.
21Ka kula kada ka juya ga mugunta,
abin da ka fi so fiye da wahala.
22“An ɗaukaka Allah cikin ikonsa.
Wane ne malami kamar sa?
23Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi,
ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’
24Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa,
waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa.
25Dukan’yan adam sun gani;
mutane sun hanga daga nesa.
26Allah mai girma ne,
ya wuce ganewarmu!
Yawan shekarunsa ba su bincikuwa.
27“Yana sa ruwa yă zama tururi
yă zubo daga sama.
28Gizagizai suna zubo da raɓarsu
kuma ruwan sama yana zubowa’yan adam a wadace.
29Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai
yadda yake tsawa daga wurin zamansa?
30Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi,
tana haskaka zurfin teku.
31Haka yake mulkin al’ummai
yana kuma tanada abinci a wadace.
32Yana cika hannuwansa da walƙiya
kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi.
33Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa;
ko shanu sun san da zuwansa.
Copyright information for
HauSRK